Yemen: Mutane 7 Sun Mutu Sanadiyyar Harin Jiragen Yakin Saudiyya
Mai magana da yawun sojojin kasar Yemen Yahya al-sari'i ya bayyana cewa akalla mutane 7 ne su ka rasa rayukansu sanadiyyar wani hari da jiragen yakin Saudiyya su ka kai a yammacin kasar
Tashar talabijin din al-masirah ta kasar Yemen ta ambato kakakin sojan kasar, Yahya Sari'i yana cewa; Harin da Jiragen yakin Saudiyyar su ka kai, yana a karkashin keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a yankin Hudaidah ne da kawancen Saudiyya ke ci gaba da yi
Kakakin sojan na Yemen ya kuma kara da cewa; mayaka 'yan koren Saudiyya sun kuma yi amfani da manyan bindigogi da kuma gurneti akan gidajen fararen hula da gonakin noma a yankin al-Hudaidah.
A yankin al-fazah ma da ke kudancin gundumar Hudaidai jiragen yakin na Suadiyyar sun kai wasu hare-haren da su ka yi sanadiyyar mutuwar mace guda da kananan yara biyu
An cimma yarjejeniyar tsagaita wutar yaki ne a yankin Hudaidai a kasar Sweeden, da dukkanin bangarorin da suke yaki da juna a Yemen suka rattaba hannu
Sai dai a cikin kasa da wata guda mayakan kawancen da Saudiyya take jagoranta sun keta yarjejeniyar a lokuta da dama
Saudiyya ta shelanta yaki akan kasar Yemen tun a 2015 ne wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan mutane fiye da 13,000