Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kai Hari A Babban Birnin Kasar Yemen
(last modified Sun, 20 Jan 2019 06:40:26 GMT )
Jan 20, 2019 06:40 UTC
  • Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kai Hari A Babban Birnin Kasar Yemen

Da safiyar yau Lahadi ne jiragen yakin na Saudiyya suka kai hari akan babban birnin kasar Yemen, San'aa

Shedun ganin ido sun ce an kai harin ne a yankin Wadi-Ahmad da ke arewacin kasar.

Rahotannin farko da suke fitowa daga birnin sun ce ya zuwa yanzu fararen hula 2 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar harin.

Shugaban majalisar koli ta juyin juya halin kasar Yemen, Muhammad Ali al-Huthy ya ce; hare-haren na jiragen yakin kawancen Saudiyya ba su tsorata al'ummar kasar Yemen

Al-Huthy ya ci gaba da cewa; Harin da aka kai wa San'aa ya saba dokokin kasa da kasa

Saudiyya da Haaddiyar Daular Larabawa a karkashin cikakken goyon bayan Amurka sun shelanta yaki akan kasar Yemen a cikin watan Maris a 2015, tare da killace kasar ta sama da kasa da ruwa.

Dubban mutane ne su ka rasa rayukansu a sanadiyyar hare-haren na Saudiyya, tare kuma da jikkata wasu dubun dubata.