Nasrullah:Isra'ila Ta Sha Kashi A Siriya
(last modified Sun, 27 Jan 2019 06:55:14 GMT )
Jan 27, 2019 06:55 UTC
  • Nasrullah:Isra'ila Ta Sha Kashi  A Siriya

Shugaban kungiyar hizbullah ta kasar Labnon ya ce haramtacciyar kasar Isra'ila ta sha kashi a kasar Siriya

Yayin da yake tattaunawa da tashar talabijin din Almayadeen ta kasar Labnon a daren jiya assabar, shugaban kungiyar hizbullah sayyid hasan nasrullah ya yi ishara nasarar baya-bayan nan da kungoyoyin gwagwarmaya suka samu a kan 'yan ta'adda musaman ma a Siriya, inda ya ce a halin da ake ciki yanzu, haramtacciyar kasar Isra'ila ta sha kashi a kasar Siriya, sannan ya ce duk wani fata da Isra'ilan ke da shi a Siriya ya rushe

Sayyid Nasrullah ya ce a halin yanzu kurdawa na cikin hali mai kyau da ba samu kamarsa ba a tsahon shekaru takwas da suka gabata.

A yayin da yake ishara kan shirin da sahayunawa ke da shi a kan iyakokin kasar Labnon, Sayyid Hasan Nasrullah ya ce matukar dai Sahayunawa suka kuskure suka kawo wa Labnon hari, to shakka babu duk wani lungu da sako na haramtacciyar kasar Isra'ila zai kasance filin daga, domin a halin da ake ciki yanzu, kungiyar Hizbullah ta mallaki makamai masu linzami da suke da karfin kai hari a ko wani lungu na haramtacciyar kasar Isra'ila, sannan ya gargadi mahukuntan Isra'ila da kadda suyi wantar kai hari a kan wani dan kungiyar Hizbullah, a kasar Labnon ne ko a kasar Siriya, domin za a mayar musu da martani mai tsanani.

A yayin da ya koma kan rikicin Palastinu,da shirin Amurka na yarjejjeniyar Karni, sayyid Hasan Nasrullah ya ce babu wata kungiya ko gungun Palastinu da zai amince da wannan shiri.sannan ya ce duk da kokarin da Amurka gami da Muhamad bn salman yariman kasar Saudiya ke yi na ganin wannan yarjejjeniya ta wakana a aikace, amma abin ya cutura kuma ba za su nasarar har abada ba.