Harin Bam Ya Yi Ajalin 'Yan Sanda Hudu A Iraki
(last modified Sun, 27 Jan 2019 10:47:23 GMT )
Jan 27, 2019 10:47 UTC
  • Harin Bam Ya Yi Ajalin 'Yan Sanda Hudu A Iraki

Rahotanni daga Iraki na cewa jami'an 'yan sanda hudu ne suka rasa rayukansu a wasu jerin hare haren bam a arewacin Bagadaza.

Majiyoyin 'yan sanda sun ce harin na farko ya auke ne a wajen wani shingen bincike na jmia'an 'yan sanda dake lardin Sharkat a arewacin Bagadaza babban birnin kasar, inda 'yan sanda biyu suka mutu kana wasu takwas suka raunana.

Harin na biyu kuma ya wakana ne a daidai lokacin da wani ayarin masu aikin ceto ya dsohi yankin, inda nan kuma harin ya hallaka  'yan sanda biyu da kuma raunata wasu uku.

A shakara 2017 ne gwamnatin Iraki ta sanar da murkushe 'yan ta'adda na IS, a sassan kasar, to saidai har yanzu ana fusknatar barazanar 'yan ta'adda da sukayi kaka-gida a wasu yankuna musamman wadanda suka hada da yankin hamada da tsaunuka.

Ko a ranar Alhamis data gabata ma, wani harin bam da aka kai da mota ya yi sanadin mutuwar dan sanda guda a lardin Hawija, shi ma wani yanki da aka kwato daga hannun 'yan ta'addan na IS.