Palasdinawa Biyu Sun Yi Shahada
Rahotanni da suke fitowa daga Palasdinu da ke karkashin mamaya sun ce; Palasdinawa biyu sun yi shahada ne sanadiyyar harbinsu da sojojin sahayoniya su ka yi a garin Yafa
Palasdinawan biyu su ne Ramzy Majid Hammad dan shekaru 23 da aka harbe shi a garin Yafa kusa da Tel Aviv, ya kuma yi shahada ne jim kadan bayan kai shi asibiti
Sai kuma Hasib Musa dan shekaru 60 wanda sojojin Sahayoniya su ka harbe shi a garin Nasirah wanda shi ne ya cika bayan kai shi asibitin garin Haifah
Kawo ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayani akan dalilin harbin Palasdinawan biyu da 'yan sayahoniya su ka yi.
Palasdinawan da suke cikin yankunan dake karkashin mamaya, suna fuskantar takurawa daidai da wadanda suke a cikin yankin Gaza