Rasha : Wajibi Ne Gwamnatin Syria Ta Shimfida Ikonta A Fadin Kasar
(last modified Thu, 31 Jan 2019 12:14:47 GMT )
Jan 31, 2019 12:14 UTC
  • Rasha : Wajibi Ne Gwamnatin Syria Ta Shimfida Ikonta A Fadin Kasar

Wakilin kasar Rasha a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ne ya bayana haka a jiya laraba

Vasily Nebenzya ya ce; Tun da fari Rasha ta jaddada cewa; Hanya mafi dacewa ta kawo karshen matsalar yankunan da 'yan ta'adda suke cikinsu, shi ne gwamnatin Syria ta shimfida ikonta a cikinsu.

Bugu da kari wakilin kasar ta Rasha a Majalisar Dinkin Duniyar ya yi ishara da batun sulhu a kasar Syria, sannan ya kara da cewa: " Ana ci gaba da tuntubar juna a tsakanin Rasha Iran da Turkiya da kuma gwamnatin Damascus sannan da Majalisar Dinkin Duniya domin fara aikin kwamitin da zai rubuta tsarin mulkin kasar Syria a Geneva.

Babban jami'in diplomasiyyar kasar ta Rasha a Majalisar Dinkin Duniya ya kuma ja kunnen kasashen turai akan kokarin da suke yi na cusawa wakilin Majalisar Dinkin Duniya akan kasar Syrai ra'ayinsu tare da cewa hakan ba zai taimaka wa zaman lafiya ba

Kasar Syria dai ta fada cikin matsalolin tsaro ne a 2011 da 'yan ta'adda masu samun goyon bayan kasashen turai, Amurka da larabawa, su ka shelanta yaki akan gwamnati da al'ummar kasar.

Sai dai gwamnatin Syria tare da taimakon kawayenta sun sami galaba akan 'yan ta'addar.