Sojojin Hayar Saudiya Sun Fada Tarkon Dakarun Tsaron Yemen
(last modified Sat, 02 Feb 2019 07:19:51 GMT )
Feb 02, 2019 07:19 UTC
  • Sojojin Hayar Saudiya Sun Fada Tarkon Dakarun Tsaron Yemen

Sojojin hayar Saudiya da dama ne suka hallaka bayan fadawa tarkon dakarun tsaron yemen a kudancin Saudiya

Cikin wani rahoto da ta bayar a daren jiya juma'a, tashar talabijin din Almasira ta habarta cewa sojojin hayar saudiya sun fada tarkon dakarun tsaron yemen a kusa da tsauni  Alkais na jihar Jizan dake kudancin Saudiya.

A bangare guda sojoji da dakarun sa kai na kasar yemen din sun yi barin wuta a matattarar jami'an tsaron saudiya a kusa da kofar Alab na jihar Asir dake kudancin saudiya a daren jiya juma'a.

Kawo yanzu dai,  ba a bayyana irin hasarar rayuka ko dukiya da aka yi sanadiyar wannan farmaki.

Tun a watan Maris din 2015 kasar Saudiya bisa cikekken goyon bayan Amurka da hadaddiyar daular larabawa da wasu kasashen Larabawa da Turai ta fara kai harin wuce gona da iri kan Al'ummar kasar Yemen tare da killace kasar, ta ruwa, da kasa da sararin samaniya.

Ya zuwa yanzu dai yakin ya salwanta rayukan yamaniyawa  fiye da dubu 14 tare da jikkata wasu dubai na daban da kuma raba wasu milyoyi da mahalinsu bisa gididdigar Majalisar Dinkin Duniya.