MDD Na Tattaunawa Da Bangarorin Dake Rikici A Yemen
(last modified Sun, 03 Feb 2019 09:44:11 GMT )
Feb 03, 2019 09:44 UTC
  • MDD Na Tattaunawa Da Bangarorin Dake Rikici A Yemen

Jagoran masu sanya ido na MDD, a birnin Hodeida, ya hada wakilan bangarorin dake rikici a Yemen, a wani mataki na daddale yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a yankin.

Tattaunar wacce Janar Patrick Cammaert ke jagoranta na gudana ne a cikin wani jirgin ruwa na MDD, a gabar ruwan Hodeida.

A cen baya dai an kasa yin ganawar, kasancewar 'yan Houtsis sun ki amince shiga tattaunawar a wani yanki dake karkashin gwamnatin Yemen.

Tattaunawar ta yau Lahadi, ita ce ta uku, kuma a cewar MDD zata maida hankali kan yadda za'a aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a Sweden wacce ta tanadi yadda bangarorin zasu janye dakarunsu a yankin na Hodeida domin bada damar gudanar da ayyukan jin kai.

Alkalumman da MDD, ta fitar sun nuna cewa, rikicin kasar ta Yemen, ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 10,000 tun bayan da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kaddamar da yakin ba gairi ba dalili kan kasar ta Yemen, lamarin da kuma ya jefa kasar cikin bala'i mafi muni a duniya inji MDD.