Paparoma Francis Na Ziyarar Farko A Hadaddiyar Daular Larabawa
Jagoran darikar 'yan katolika, Paparoma Francis, zai fara wata ziyara yau Lahadi a Hadaddiyar Daular Larabawa, wacce ita ce irinta ta farko ta wani Paparoma.
Bayan irin wannan ziyara da ya kai a shekara 2014 a Turkiyya, sannan a Masar a shekaru biyu da suka gabata, Fafaroma Francis zai fara ziyara ta kwanaki a hadaddiyar daular larabawa, nada nufin kirabn hadin kan addinai akan zaman tare.
Baya ga Hadaddiyar Daular Larabawa Fafaroma zai kai irin wannan ziyara a kasar Morocco a cikin watan Maris mai zuwa.
Hadadiyar Daular Larabwa dai na kunshe da mabiya addinin krista kashi 10% wadanda galibinsu 'yan rani ne dake aiki a kasar wadanda suka fito daga kasashen Indiya da kuma Philippines.
Yarima mai jiran gado na Hadaddiyar Daular Larabawan ne, Shaikh Mohammed ben Zayed al-Nahyane, da kuma karamar cocin katolika ta birnin Abou Dhabi suka gayyaci Paparoman.
A yayin ziyarar an tsara Paparoman zai gana da manyan malaman addinin Islama, da na Buda, da yahudawa da kuma Hindu, da kuma yarima mai jiran gado na kasar, duka a yunkurin samar da zaman lafiya da fahimtar juna.