Kasar Morocco Ta Kira Jakadanta A kasar Saudia Zuwa Gida.
(last modified Fri, 08 Feb 2019 19:16:00 GMT )
Feb 08, 2019 19:16 UTC
  • Kasar Morocco Ta Kira Jakadanta A kasar Saudia Zuwa Gida.

Jakadan kasar Morocco a birnin Riyad ya bada sanarwan cewa an bukace shi ya koma gida sanadiyyar sabani da ke kara tsanani tsakanin Rabat da- Riyad

Kamfanin dillancin labaran Anatoly ya nakalto Mustafa Al-Mansuri yana fadawa tashar talabijin ta Al-Arabia mallakin kasar ta saudia kan cewa kwanaki ukku da suka gabata ne aka bukace shi da ya koma gida sanadiyyar kara tabarbarewar dangantaka tsakanin kasarsa da kasar Saudia.

Har'ila yau a ranar Alhamis da ta gabata ce jaridun kasar ta Morocco suka bada labarin cewa gwamnatin kasar ta janye daga kawancen yaki da kasar Yemen karkashin jagorancin kasar Saudia. 

Dangantaka tsakanin Rabat da kuma Riyad ta fara tsami ne tun lokacinda gwamnatin kasar Morocco ta bayyana goyon bayanta ga kasar Qatar a takaddar da ta shiga tsakaninta da kasar Saudia.

A cikin watan Nuwamban shekara ta 2018 da ta gabata ma, gwamnatin kasar Morocco ta ki amincwa da ziyarar yerime mai jiran gadon sarautar kasar Saudia Muhammad Bin Salman zuwa kasar ta Morocco sanadiyar kisan Jamal Khashaggi dan jaridan nan mai adawa da gwamnatin kasarsa.