Jam'iyyun Siyasar Iraki Suna Son Ganin Ficewar Sojojin Amurka Daga Kasarsu
(last modified Tue, 12 Feb 2019 07:09:04 GMT )
Feb 12, 2019 07:09 UTC
  • Jam'iyyun Siyasar Iraki Suna Son Ganin Ficewar Sojojin Amurka Daga Kasarsu

Kawancen jam'iyyun siyasar Iraki na "Fatah' da kuma "Sa'irun' sun bayyana wajabcin ficewar sojojin Amurka daga cikin kasar

A wani taron manema labaru da kawancen jam'iyyun biyu na Sa'irun karkashin jagroancin Muqtada Sadar, da kuma Fatah a karkashin Hadi al-Amuri, sun bayyana cewa; suna adawa da ci gaba da zaman sojojin Amurka a cikin kasar

Hadi Amuri ya ce; Wajibi ne Amurka ta tattara ya nata, ya nata domin ficewa daga cikin kasar da gaggawa

A gefe daya, Mahdi Taqi, wanda memba ne a kwamitin tsaro na Majalisar dokokin Iraki, ya bayyana cewa;  ya zuwa yanzu 'yan majalisa 70 sun rattaba hannu akan daftarin kudurin da za a gabatar da shi a Majalisar domin amincewa da ficewar Amurka daga cikin kasar

Amurka ta fice daga cikin Iraki a 2011, bayan da ta kasa samun goyon bayan gwamnatin kasar na ta ci gaba da girke sojojinta a Irakin. Sai dai ta sake komawa cikin Iraki a 2014 da sunan fada da ayyukan ta'addanci

A cikin watannin bayan nan batun ci gaba da zaman sojojin Amurka a Iraki ya zama batun da 'yan siyasar kasar suke tattaunawa domin kawo karshensa.