Sojojin Sahayoniya Sun Kai Hari A Yankin Qunaidhara Na Kasar Syria
A daren jiya Litinin ne sojojin Sahayoniyar su ka kai hari a gundumar Qunaidhara ta kasar Syria ta hanyar amfani da tankokin yaki da kuma manyan bindigogi
Kamfanin dillancin labarun kasar Syria "Sana" ya ba ba labarin cewa; Babu asarar rayuka a sanadiyyar harin na 'yan sahayoniya
Rahoton ya ci gaba da cewa; "Yan sahayoniyar sun kai hare-haren ne a yankin Tallul-Dar'iyyah, da kuma Jabatal-Khashbi da suke a gundumar ta Qunaidharah
Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta kasance a gaba-gaba wajen taimakawa 'yan ta'adda a kasar Syria ta hanyar basu makamai da kuma kai wa sojojin Syria hare-hare.
Ricikin Syria ya fara ne a 2011 da kungiyoyin 'yan ta'adda masu samun goyon bayan Amurka da HKI da kuma wasu kasashen turai da kuma larabawa, su ka fara kai hare-hare a sassa daban-daban na kasar
Sojojin Syria tare da kawayenta da su ka hada da jamhuriyar Musulunci ta Iran sun sami nasara akan 'yan ta'addar ta hanyar murkushe su.