Yemen: Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kashe Masunta 8 A Garin Hudaidah
Jiragen yakin Saudiyyar sun kai harin ne akan kananan kwale-kwale na kamun kifi a garin Hudaidah a yau Laraba
Tashar talabijin din al-masirah ta ba da labarin cewa; Baya ga masunta 8 da su ka kwanta dama, sanadiyyar harin da jiragen yakin Saudiyya, wasu masuntan biyar sun jikkata
Bugu da kari jiragen yakin na Saudiyya sun kai wasu hare-haren a garin Budhai da ke gundumar ta Hudaidah
Rahotannin farko sun ce ya zuwa yanzu mutane 10 ba a san makomarsu ba sanadiyyar harin.
Sojojin Saudiyya suna zargin kawancen yakin da Saudiyya take jagoranta da keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a yankin Hudaidah.
Garin Hudaidah yana da muhimmanci saboda tashar jiragen ruwan da take cikinsa wacce ake shigar da mafi yawancin kayan agaji zuwa cikin kasar.
Saudiyya ta shelanta yaki ne akan kasar Yemen tun a 2015 wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan mutane fiye da 13,000