Hamas: 'Yan Sahayoniya Ne Kadai Su Ka Amfana Daga Taron Warsaw
Wani babban jigo a kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas Usama Hamadan ne ya bayyana haka sannan ya kara da cewa; Taron zai kara yawan matsalolin da yankin gabas ta tsakiya yake da su ne
Usama Hamadan ya kuma kara da cewa; Abin da taron na Warsaw yake son cimmawa shi ne samar da sauyi a yankin gabas ta tsakiya domin ya dace da manufofin 'yan sahayoniya
Shi kuma kakakin kungiyar ta Hamas Hazim Kasim ya bayyana cewa; Taron na Warwaw bai isa ya danne hakkokin al'ummar Paladinu ba, domin 'yan sahayoniya sune makiya na asali wadanda suke a matsayin barazan ga tsaro da zaman lafiya na gabas ta tsakiya
Kakakin na kungiyar Hamas ya kuma kara da cewa; A Palasdinu ne za a dauki mataki akan makomar Palasdinu ba a Warwar babban birnin Poland ba.
A jiya Laraba ne aka bude taron da Amurka ta shiya a birnin Warsaw domin tattauna abubwan da suke faruwa a gabas ta tsakiya da kuma kokarin samar da sauyi da zai dace da manufar 'yan sahayoniya