Kawancen Saudiya Ya Hallaka Mata Da Kananen Yara A Yemen
Cikin wani sabon ta'addanci, jiragen yakin kawancen saudiya sun kai hari a jihar Hajjah dake arewa maso gabashin kasar yemen tare da kashe fararen hula 6.
Kamfanin dillancin labarai na gidajen rediyo da talabijin na kasar Iran ya habarta cewa jiragen yakin kawancen saudiya sun kai wasu sabin hare-haren ta'addanci a kan gidajen fararen hula, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 6, mata 4 kananen yara biyu tare kuma da raunana wasu uku na daban.
A matsayin mayar da martani, Sojoji da dakarun sa kai na kasar ta yemen, sun kai farmaki kan wuraren taruwar sojojin hayar saudiya a lardin Aham da wasu yankuna na jihohin Jizan daAsir tare kuma da halba musu makami mai Linzami samfarin zilzal na daya, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka da jikkatar sojojin hayar na saudiya da dama.
A nata bangare tashar talabijin din Al-alam ta bayar da rahoton cewa limamai da maliman garin Alhudaida na kasar yemen sun yi tofin alatsine kan kasashen dake kai musu harin wuce gona da iri da kuma karye yarjejjeniyar tsagaita wutar da aka yi a birnin Sweden, tare da tabbatar da goyon bayansu ga sojoji da dakarun sa kai na kasar.