Masar Ta Bude Wa Musulmin Gaza Hanya Don Yin Aikin Umara
Kasar Masar ta bude wa musulmin Gaza mashigar Rafah domin isa kasar, da nufin wucewa zuwa Saudiyya don gudanar da aikin umura.
Rahotanni sun nuna cewa musulmin zirin gaza kimanin 800 ne suka bi ta mashigar Rafah zuwa, bayan da suka samu takardar visa daga hukumoin kasar Masar.
Bayanai sun nuna cewa a cikin ko wace shekara kimanin mutanen Gaza 2,500 ne ake baiwa damar fita daga zirin na Gaza ta kasar Masar, domin gudanar da aikin hajji a Makka, amma wannan kuma shi ne karo na farko tun bayan shekara 2014 da aka budewa musulmin na Zirin Gaza mashigar don samun isa Saudiyya domin gudanar da aikin umara.
Zirin Gaza wanda ke tsakanin Isra'ila da tekun Mediranean da kuma Masar, ya kasance tsawan shekaru sama da goma karkashin ikon Isra'ila, lamarin da ya kasance tsawan wadanan shekarun babban kalubale wa musulmin na Gaza, domin fita daga yankin.