Mar 07, 2019 04:48 UTC
  • Kasar Habasha Ta Taimaka Wajen Warare Rikicin Kasashen Kenya Da Somaliya

Sakamakon shiga tsakani wanda Fira ministan kasar Habasha Abiy Ahmad ya yi a rikicin kasashen Somaliya da Kenya, kasashen biyu sun sami fahimtar juna.

Ofishin Fira ministan kasar Habasha Abiy Ahmad ya fitar da sanarwa wacce  a ciki ya bayyana cewa;  shiga tsakanin ya haifar da da, mai ido, kuma shuwagabannin kasashen biyu sun amince su kawo karshen sabanin da ke tsakaninsu.

Fira ministan kasar ta Habasha ya isa kasar Kenya a tare da shugaban kasar Somaliya inda su ka gana da shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta.

A gefe guda kuma , ofishin shugaban kasar Somaliya ya fitar da bayani wanda a cikisa ya godewa kasar Habasha saboda shiga tsakanin da ta yi don warware sabanin dake tsakaninta da Kenya.

Kimani wata guda da ya gabata ne, Kasar Kenya ta kira yi jakadanta daga kasar Somaliya domin nuna kin amincewa da matakin da Mogadishu ta dauka na fara hako man fetur da iskar gas a wani yanki na kan iyakar ruwa da kasashen biyu suke da sabani a kansa