Mar 13, 2019 05:38 UTC
  • An Fara Taron Goyon Bayan Siriya A Birnin Brussels

Kungiyar Tarayyar Turai na wani taro, a birnin Brussels, kan batun kasar Siriya ‘’mai taken goyon baya ga makomar siriya da yankin.

Taron wanda aka fara a jiya Talata na hadin gwiwa ne tsakanin kungiyar EU da MDD, mai taken goyon baya ga makomar siriya da yankin nada nufin warware rikicin siyasar kasar da kuma farfado da tattalin arzikinta da bunkasa yankin gabas ta tsakiya.

Fiye da mutum dubu daya suka halarci wannan taro, wanda shi ne karo na uku, wanda suka hada da wakilan kungiyoyin fararen hula na Siriya da yankin, ministoci na kasashe makwabtan siriya da masu ruwa da tsaki kan harakokin tattalin arziki na kasa da kasa da kungiyoyin kasa da kasa gami da na agaji.

Ministan harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran, Muhamad Javad Zarif, shima ya halarci wannan taro mai taken Brussels na uku.

A yayin bude tare, Helga Maria mataimakiyar babbar jami'ar dake kula da harkokin siyasar wajen kungiyar tarayyar turai ta ce kungiyar EU ta dauki alkawarin warware  matsalolin kasar Siriya da kuma kawo karshen bala'in da al'ummar kasar suke ciki.

Misis. Schimid ta kara da cewa wannan taro zai fi mayar da hankali ne kan yadda za a samar da ayyukan yi ga matasan siriya, da kuma magance matsalar 'yan gudun hijra gami da tabbatar da tsaro a wasu yankunan kasar.