Mar 13, 2019 16:41 UTC
  • Jami'an Tsaron Isra'ila Sun Kai Farmaki Kan Yara 'Yan Makarantar Palastinu

Jami'an tsaron Sahayuna sun kai farmaki kan wata makarantar Firamire a garin Alkhalil na yankin Palastinu

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto kafar watsa labaran Palastinu wato Palastinu Alyaum na cewa a wannan Laraba jami'an tsaron Sahayuna sun kai farmaki wata  makarantar firamire a garin Alkhali tare da harba yanaki mai sanya hawaye, lamarin da ya yi sanadiyar suma na wani malami guda  tare da yara  'yan makaranta da dama.

Har ila yau jami'an tsaron sahayunan sun rika bin  yara 'yan makarantar da motoci masu sulke a harabar makarantar, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar yara 'yan makarantar da dama. 

Rahoton ya ce wannan farmaki, ya sanya fargaba da tsoro a zukatan yara 'yan makarantar, lamarin da ya sanya aka rufe makarantar a yau.

A bangare guda, Hisam Badran gungu a kungiyar Hamas ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa kungiyoyin gwagwarmaya ba za su zura ido suna kallon irin cin kashin da Jami'an tsaron sahayuna suke aiwatarwa kan Kananen yaran Palastinawa don haka, za su dauki matakin mayar da martani nan gaba.