Sojojin Isra'ila Sun Kame Babban Limamanin Masallacin Quds
Sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi awon gaba da babban limamin masallacin Quds mai alfarma.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, jim kadan bayan kammala sallar Juma'a a jiya, sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila sun kame sheikh Muhammad Salim, suka tafi da shi wani wuri da ba a sani ba.
A hudubar Juma'a da ya gabatar jiya a masallacin Quds mai alfarama, Sheikh Muhammad salim ya soki yahudawan Isra'ila kan cin zarafin wurare masu tsarki da suke yi, tare da jaddada cewa hakan lamari ne da al'ummar musulmi ba za su taba yin shiru a kansa ba.
A ranar Alhamis da ta gabata ce kimanin yahudawan Sahyuniya 1000 suka afka kan makabartar annabi Yusuf (AS) da ke garin Nablus, inda suka keta alfarmar wannan wuri mai daraja, wanda kuma a nan ne kabarin Annabi Yusuf (AS) yake.