Staffan de Mistura Ya Gana Da Jami'an Gwamnatin Syria A Yau
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i3760-staffan_de_mistura_ya_gana_da_jami'an_gwamnatin_syria_a_yau
Babban manzon musamman na majalisar dinkin duniya mai shiga tsakani kan rikicin Syria Staffan de Mistura ya gana da jami'an gwamnatin Syria a yau a birnin Damascus.
(last modified 2018-08-22T06:58:07+00:00 )
Apr 11, 2016 12:03 UTC
  • Staffan de Mistura Ya Gana Da Jami'an Gwamnatin Syria A Yau

Babban manzon musamman na majalisar dinkin duniya mai shiga tsakani kan rikicin Syria Staffan de Mistura ya gana da jami'an gwamnatin Syria a yau a birnin Damascus.

A lokacin da yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar ta Syria Walid Mu'allima yau, Staffan de Mistura ya bijiro da batun ci gaba da tattaunawa tare da bangarorin 'yan adawar siyasa da kuma gwamnatin Syria a Geneva a ranar 13 ga wannan wata na Afirilu.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen Syria ya bayyan amasa cewa, a kowane lokaci su a shirye suke domin tattaunawa, babbar matsalar ita ce, su 'yan adawa ba su da wani kudiri na siyasa a hannunsu, sai dai kudirin da kasashen da suke daukar nauyinsu suka dauka a kansu.

Ya kara da cewa yanzu haka wasu daga cikin kasashen da suke daukar nauyin 'yan adawar siyasa na Syria, su ne kuma a bangare guda suke daukar nauyin 'yan ta'adda, inda ya yi ishara da sabbin makaman da kasashen Saudiyya da Turkiya suka bai wa ISIS da Nusra domin kara tsananta hare-hare a cikin kasar Syria.