Farashin Fetir Ya Sake Faduwa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4045-farashin_fetir_ya_sake_faduwa
Farashin man fatir ya sake faduwa a kasuwannin duniya da kashi 5,45% bayan taron kasashe masu arzikin man ya watse ba tare da cimma wata matsaya ba.
(last modified 2018-08-22T06:58:09+00:00 )
Apr 18, 2016 05:27 UTC
  • Farashin Fetir Ya Sake Faduwa

Farashin man fatir ya sake faduwa a kasuwannin duniya da kashi 5,45% bayan taron kasashe masu arzikin man ya watse ba tare da cimma wata matsaya ba.

Tattaunawar kasahen na OPEC ta fuskanci koma baya ne saboda kace-nace tsakanin kasashen Saudiyya da Iran.

Iran dai ta kauracewa taron na Doha ne saboda a cewar ta bashi da wata fa'ida gare ta, yayin da Saudiyya ke cewa ba zata rage yawan man da take hakowa ba, mudin Iran bata yi hakan ba.