Hollande Na Ziyara A Kasar Jodan
Apr 19, 2016 04:39 UTC
Yau Talata shugaba Farancois Hollande ya isa kasar Jodan a ziyarasa da zata maida hankali kan matsalar 'yan gudun hijira da kuma yaki da 'yan ta'adan (IS)
Wannan ziyara ta yini guda na zamen ta karshe a ran gadin kwanaki hudu da shugaba Hollande ya kaddamar a yankin gabas ta Tsakiya, bayan wace ya kai kasashen Labonan da kuma Masar.
kasar Jodan dai na karbar 'yan gudun hijira Syria sama da 600,000.