Afganistan : Bam Ya Kashe Mutane 28 A Kabul
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4078-afganistan_bam_ya_kashe_mutane_28_a_kabul
Rahotanni daga Afganistan na cewa akalla mutane 28 ne suka rasa rayukan su a harin da kungiyar Taliban ta dauki alhakin kaiwa a birnin Kaboul.
(last modified 2018-08-22T06:58:09+00:00 )
Apr 19, 2016 05:03 UTC
  • Afganistan : Bam Ya Kashe Mutane 28 A Kabul

Rahotanni daga Afganistan na cewa akalla mutane 28 ne suka rasa rayukan su a harin da kungiyar Taliban ta dauki alhakin kaiwa a birnin Kaboul.

Harin da aka kai da wata mota a wannan safiyar yayi kuma jikkata mutune sama da 200.

Wasu rahotanni na daban sun ce an yi ta harbe-harbe daga bisanin harin, lamarin da yayi sanadin mutuwar fararen hula da dama da kuma jami'an tsaro.

An dai kai hari ne a harabar ma'aikatar tsaron kasar dake Kaboul.

Tuni dai shugaban kasar Ashraf Ghani ya fitar da sanarwar yin allawadai da wannan harin.