An Gudanar Da Taron Yin Allawadai Da Kiran Hizbullah Yan Ta'adda
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4207-an_gudanar_da_taron_yin_allawadai_da_kiran_hizbullah_yan_ta'adda
An gudanar da taron kasa da kasa a kasar Tunisia tare da bukatar yin Allawadai da kiran Hizbullah yan ta'adda.
(last modified 2018-08-22T06:58:10+00:00 )
Apr 21, 2016 22:35 UTC
  • An Gudanar Da Taron Yin Allawadai Da Kiran Hizbullah Yan Ta'adda

An gudanar da taron kasa da kasa a kasar Tunisia tare da bukatar yin Allawadai da kiran Hizbullah yan ta'adda.

An gudanar da taron kasa da kasa a kasar Tunisia tare da bukatar yin Allawadai da kiran kungiyar Hizbulla ta kasar Lebanon a matsayin kungiyar yan ta'adda. Intiwan Dau, Sakataren komitin tattaunawa tsakanin Musulmi da Kirista a kasar Lebenon, wanda ya sami halartar taron na kasar Tunisa ya ce kungiyar Hizbullah kungiya ce ta neman zaman lafiya da kuma tabbatar da sulhi ba ma a kasar Lebanon Kadai ba, har ma da kasashen yankin.

Dau, ya kara da cewa kungiyar Hizbulla kungiya ce ta kare kasar Lebanon daga Haramtacciyar kasar Israel sannan tana gwagwarmaya don nemawwa Palasdinawa 'yencinsu daga yahudawan sahyonia yan mamaya.

Daga Karshe Dau ya kammala da cewa kasashen da suke danganta kungiyar Hizbullah da ayyukan ta'addaci basu yi la'akari da maslatar kasashen yankin ba.

Har'ila Khalid Assufyani, na wata kungiyar gwagwarmaya ta Palasdinwa a kasar Morocco, wanda shi ma ya sami damar halattan taron, ya ce dukkan wakilan kasashen duniya da suka halarci taron na Tunisia sun yi All..wadai da sanya Hizbullah cikin jerin kungiyoyin yan Ta'adda a duniya.