Dan Takarar Neman Shugabancin Amurka Ya Bukaci A Binciki Saudia
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4312-dan_takarar_neman_shugabancin_amurka_ya_bukaci_a_binciki_saudia
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Democrate a kasar Amurka ya bukaci gwamnatin kasar da kuma majalisar
(last modified 2018-08-22T06:58:10+00:00 )
Apr 24, 2016 13:22 UTC
  • Dan Takarar Neman Shugabancin Amurka Ya Bukaci A Binciki Saudia

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Democrate a kasar Amurka ya bukaci gwamnatin kasar da kuma majalisar

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Democrate a kasar Amurka ya bukaci gwamnatin kasar da kuma majalisar dattawan kasar ta gudanar da bincike kan irin rawan da kasar saudia ta taka a cikin harin 11-Satuban -2001M.

Bernie Sanders, ya bayyana haka ne a yau a lokacinda yake hari da tashar television na NBC. a yau Lahadi ya kuma kara da cewa idan an gano cewa kasar saudia tana da hannu a kissan Amurkawa a harin 11/09 suna da damar shigar da kara kasar saudia a cikin kotunan kasar.

Bernie Sanders, ya kara da cewa akwai wasu shaidu da suka tabbatar da cewa kasar saudia tana amfani da kudade wajen daukar nauyin ta'addanci a kasashen duniya.

Gwamnatin kasar Saudia dai ta bayyana cewa zata saida kadarorinta a kasar Amurka idan har majalisar dokokin kasar ta bude tattaunawa kan rawan da ta taka a harin 11/09-2001. Hakama shugaban kasar ta Amurka Barak Obama ya ce zai ki sanya hannu a kan duk wata doka ta binciken kasar Saudia da ta zo ofishinsa.