Ministan Tsaro Isra'ila Ya yi Murabus
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i5434-ministan_tsaro_isra'ila_ya_yi_murabus
Ministan tsaron Israi'la ya bayana a wannan Juma'a da murabus din sa, sakamakon jayeya tsakaninsa da firiya ministan kasar Benjamin Netanyahu.
(last modified 2018-08-22T11:28:18+00:00 )
May 20, 2016 08:38 UTC
  • Ministan Tsaro Isra'ila Ya yi Murabus

Ministan tsaron Israi'la ya bayana a wannan Juma'a da murabus din sa, sakamakon jayeya tsakaninsa da firiya ministan kasar Benjamin Netanyahu.

Mr Moshé Yaalon wanda ke bayyana hakan a shafinsa na tweeter, ya ce sabanin sa-in-sa da jayeya da rashin yarda tsakaninsa da Netanyahu yana mai sanar da murabus dinsa tare da nisantar duk wasu harkokin siyasa dama majalisar dokoki ta Knesset.

Sabani ya kuno kai ne tsakanin Netanyahu da Yaalon tun bayan daya mikawa Avigdor Lieberman wani dan Adawa mukamin ministan na tsaro, ya kuma baiwa Mr Yaalon ministan harkokin waje.