Sayyeed Nasarallah Ya Yabawa Komandan Hizbullah Wanda Yayi Shahada A Kwanannan
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i5461-sayyeed_nasarallah_ya_yabawa_komandan_hizbullah_wanda_yayi_shahada_a_kwanannan
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyed Hassan Nasarallah ya yabawa shaheed Mustafa badrudden
(last modified 2018-08-22T06:58:18+00:00 )
May 20, 2016 13:37 UTC
  • Sayyeed Nasarallah Ya Yabawa Komandan Hizbullah Wanda Yayi Shahada A Kwanannan

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyed Hassan Nasarallah ya yabawa shaheed Mustafa badrudden

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyed Hassan Nasarallah ya yabawa shaheed Mustafa badrudden komandan dakarun kungiyar wanda ya yi shahada a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Tashar television ta Presstv mai watsa shirye shiryenta da harshen turanci a nan Tehran ya nakalto jawabin da shugaban na Hizbullah ya gabatar a dazun nan kai tsaye, yana cewa Shaheed Badruddeen ya rike muakamai da dama a cikin kungiyar, kuma ya yi aiki tare da wanda ya gada wato Hajja Ridwan kafin ya maye gurbinsa bayan shahadarsa. Banda haka Sayyeed Nasarallah ya kara da cewa Shaheed Badrudden ya taimaka a yakin shekara ta 2006 tsakanin kungiyar da sojojin HKI .

Har'ila yau shaheed Badrudden ne shugaban jami'an tsaron kungiyar da suke yakar yan ta'adda a kasar Syria har zuwa shahadarsa a cikin makon da ya gabata. Badrudden dai dan uwa ne ga shaheed Imad Mugnia shugaban kungiyar dakarun kungiyar ta huzbullah.