Harin ta'addanci ne ya kado jirgin fasinjan kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i5710-harin_ta'addanci_ne_ya_kado_jirgin_fasinjan_kasar_masar
Wata kotu a Masar ta ce jirgin fasinjan kasar da ya fado an kai masa harin ta'addanci ne.
(last modified 2018-08-22T06:58:20+00:00 )
May 24, 2016 07:58 UTC
  • Harin ta'addanci ne ya kado jirgin fasinjan kasar Masar

Wata kotu a Masar ta ce jirgin fasinjan kasar da ya fado an kai masa harin ta'addanci ne.

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ambato wata majiyar shari'ar kasar masar na cewa; Bisa la'akari da sassan jikin wasu matafiya da aka samu, da akwai yiyuwar an kai harin ta'addanci ne.

Majiyar Kotun kasar ta Masar din ta kuma ce; jirgin saman ya tarwaste ne kuma ya fadi a cikin sassa daban-daban na ruwan Metrenia. Hakan, in ji kotun yana nuni ne da yadda jirgin ya tarwatse a sama tun kafin ya fada kan ruwa.

Mutane 66 ne dai su ka rasa raukansu a hatsarin.