Sojojin Yemen Sun Hallaka Wasu Sojojin Hayan Saudiyya A Sana'a
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i5815-sojojin_yemen_sun_hallaka_wasu_sojojin_hayan_saudiyya_a_sana'a
Sojojin kasar Yemen tare da dakarun sa kan kasar sun sami nasarar dakile wani kokari na wasu sojojin hayan Saudiyya na shiga babban birnin kasar Sana'a inda suka hallaka wasu daga cikinsu.
(last modified 2018-08-22T06:58:20+00:00 )
May 27, 2016 00:27 UTC
  • Sojojin Yemen Sun Hallaka Wasu Sojojin Hayan Saudiyya A Sana'a

Sojojin kasar Yemen tare da dakarun sa kan kasar sun sami nasarar dakile wani kokari na wasu sojojin hayan Saudiyya na shiga babban birnin kasar Sana'a inda suka hallaka wasu daga cikinsu.

Tashar talabijin din Al-Masira ta kasar Yemen din ta bayyana cewar a yammacin jiya Alhamis sojojin kasar da suke samun daukin dakarun sa kai sun sami nasarar fatattakan wasu sojojin haya na kasar Saudiyya da suka yi kokarin shigowa wani yanki na gabashin birnin Sana'a inda suka hallaka mutane 20 daga cikinsu baya ga wadanda kuma suka raunata.

A bangare guda kuma jiragen yakin Saudiyya da kawayen nata sun ci gaba da ruwan bama-bamai a yankuna daban-daban na kasar Yemen din da suka hada da garin Al-Jauf da ke arewa da Ta'iz da Lahaj da ke kudu masu yammacin kasar ta Yemen inda suka kashe da kuma raunata wani adadi na mutanen wadannan garuruwan.

Cibiyoyi da 'yan siyasa daban-daban na duniya suna ci gaba da irin wannan wuce gona da iri da Saudiyyan take yi a kasar ta Yemen da sunan kokarin dawo da korarren shugaban kasar Abdurrab Mansur Hadi lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutanen kasar.