Rijiyoyin Man Assaura sun dawo kalkashin ikon Gwamnatin Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i6967-rijiyoyin_man_assaura_sun_dawo_kalkashin_ikon_gwamnatin_siriya
Rijiyoyin Man Assaura dake yammacin garin Rikka da kuma ya kasance kalkashin mamayar 'yan ta'adda ya dawo kalkashin ikon Gwamnatin Siriya.
(last modified 2018-08-22T06:58:28+00:00 )
Jun 20, 2016 01:17 UTC
  • Rijiyoyin Man Assaura sun dawo kalkashin ikon Gwamnatin Siriya

Rijiyoyin Man Assaura dake yammacin garin Rikka da kuma ya kasance kalkashin mamayar 'yan ta'adda ya dawo kalkashin ikon Gwamnatin Siriya.

Tashar Telbijin din Al'alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa Dakarun tsaron kasar Siriya sun samun nasarar 'yanto rijiyoyin Man fetur na Assaura dake da nisan kilomita 10 daga filin sauka da tashi na jiragen Saman Attabka dake yammacin garin Arrika.

Har ila yau Dakarun tsaron na Siriya sun killace 'yan ta'adda a yankunan gabashin garin Halab.

A bangare guda 'yan ta'addar da suka yi kokarin kutsawa yankunan dake kusa da kauyan Zalakiyat na arewa maso yammacin garin Hama, a taho mu gamar da suka yi da Sojojin Gwamnati da dama daga cikin su sun hallaka yayin da wasu kuma suka jikkata.

Har ila yau Tashar Telbijin din Al'alam din ta sanar da wani gumurzu tsakanin Dakarun tsaron Siriyan da 'yan ta'adda a kusa da yankin Bahariya dake gefen birnin Damuscus.

Wani Labari daga kasar Siriya ya ce wani sojin kasar Rasha dake cikin tawagar masu kai kayan Agaji ya rasa ransa a garin Humus sanadiyar tarwatsewar wata Mota shake da bama-bamai.