MDD Na Ci Gaba Da Neman Hanyoyin Sulhu A Yemen
Feb 13, 2016 07:48 UTC
-
Ismaël Ould Cheikh Ahmed wakilin MDD kan rikicin Yemen
Batun da aka fi maida hamkali akan sa a cewar jami'in sun hada da jadawalin tattaunar.
Wakilin MDD kan rikicin kasar Yemen ya ce suna ci gaba da samar hanyoyin tattaunawa a zagaye na biyu tsakanin masu rikici a kasar Yemen.
Mr Ismaël Ould Cheikh Ahmed ya bayana cewa suna tattaunawa da bangarorin da batun ya shafa na kasar ta YEmen domin samun damar karshe ta warware rikicin kasar.
Batun da aka fi maida hamkali akan sa a cewar jami'in sun hada da jadawalin tattaunar.
A makon gobe ne ake sa ran wakilin na MDD zai isa birnin New York domin gabatarwa da kwamitin tsaro na MDD sakamakon duk tattaunawar da yayi da bangarorin biyu dake rikici a Yemen.