Yamen: Ansarullah Sun Saki Fursunonin Yaki
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i7630-yamen_ansarullah_sun_saki_fursunonin_yaki
Saboda Zuwan Salla Karaman, 'Yan Huthi Na Yamen Sun Saki Fursunonin Yaki 33
(last modified 2018-08-22T06:58:32+00:00 )
Jul 04, 2016 07:51 UTC
  • Yamen: Ansarullah Sun Saki Fursunonin Yaki

Saboda Zuwan Salla Karaman, 'Yan Huthi Na Yamen Sun Saki Fursunonin Yaki 33

Kamfanin Dillancin Labarun "Irna" na Iran ya nakalto cewa; Kungiyar Ansarullah da aka fi sani da 'yan Yamen na kasar Yamen, sun saki fursunoni 33 saboda karatowar karamar salla.

Daga shigar watan Ramadhan zuwa yanzu dai kungiyar ta Ansarullah ta saki fursunoni 716.

Fursunonin da aka saki dai sun kunshi 'yan koren Saudiyya a kasar ta Yeman. An kuwa kame su ne a fagen dagar yakin da Saudiyyar ta shelanta akan al'ummar Yamen.

An kuwa saki mutanan ne dai bisa bukatar Abdul malik Huthy, shugaban kungiyar ta Ansarullah.

Fiye da shekara guda kenan dai da Saudiyyar da kawayenta su ka shelanta yaki akan al'ummar kasar Yamen da kawo ya zuwa yayi sanadin mutuwar dubban mutane da jikkata wasu dubban.

Bugu da kari, hare-haren na Saudiyya sun jawo tsayawar ayyukan kiwon lafiya a fadin kasar.