Harin Ta'addanci A Kasar Yamen
Mota Makare da Bama-Bamai da ta tashi a Birnin Aden ta kashe mutane da dama.
Majiyar Kamfanin Dillancin Labarun ( AFP) ta ce; An kai wa filin saukar jiragen sama na Aden hari da motoci biyu masu makare da bama-bamai, da hakan yayi sanadin mutuwar mutane 6.
Majiyar filin saukar jiragen saman na Aden ta ce; Motar farko ta tarwatsa kofar shiga cikin filin sauka jiragen, saboda haka mota ta biyu ta sami damar shiga cicki.
A gefe daya, fada ya barke a tsakanin sojojin kasar da kuma maharan a cikin wani sansani da ke killace.
Kungiyar alqa'eda a tsibirin larabawa dai ta kara fadada hare-harenta a cikin Yeman, tun bayan da saudiyya ta shelanta akan wannan kasa.
Kawo ya zuwa yanzu dai dubban mutane su ke kwanta dama a kasar ta Yamen.