Ana Zaben Sanatoci A Japan
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i7879-ana_zaben_sanatoci_a_japan
Yau Lahadi al'ummar Japan ke kada kuri'a domin zaben sanatoci, zaben da ake ganin zai baiwa jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta firayi ministan Shinzo Abe gagarimin rinjaye.
(last modified 2018-08-22T06:58:34+00:00 )
Jul 10, 2016 01:18 UTC
  • Ana Zaben Sanatoci A Japan

Yau Lahadi al'ummar Japan ke kada kuri'a domin zaben sanatoci, zaben da ake ganin zai baiwa jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta firayi ministan Shinzo Abe gagarimin rinjaye.

Ana ganin dai jam'iyya mai mulki zata iya samun gagarimin rinjaye a majalisar duk da siyasar Mr Abe da kuma yunkurinsa na yin gyaran fuska wa kundin tsarin mulkin kasar musamman kan ayar doka mai lamba 9 data shafi kaucewa duk wani yaki har abada.

Sama da al'umma kasar miliyan 106,6 ke kada kuri'a a zaben wanda shi ne irinsa na farko da ya baiwa matasa 'yan shekaru 18 zuwa 19 yin zaben maimakon shekara 20.

Da misalin karfe bakwai na safiyar nan ce aka bude runfunan zaben da yawan su ya kai 48,000 har zuwa karfe takwas na dare.