An Koma Yakar IS Tun Daga Turkiyya
Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar a wannan Lahadi cewa, kawacen yaki da kungiyar 'yan ta'ada na IS ya koma bakin aikinsa tun daga Turkiyya bayan dakatarwa saboda yunkurin juyin mulkin ba baiwi nasara ba.
kakakin ma'aikatar ta Pantagon Peter Cook ne ya sanar da hakan tare da cewa kawacen ya koma bakin aikinsa na yaki da kungiyar 'yan ta'adan na IS tun daga sansanonin Amurka dake Turkiyya.
Sanarwar ta ce kawacen ya koma aikinsa bayan bude sararin samaniya kasar ta Turkiyya ga jiragen yakin soji.
Turkiyya dai ta dakatar da aiki da sararin samaniyar ta ga dukkan jiragen soji bayan juyin mulkin da baiyi nasara ba a ranar Juma'a data gabata.
Amurka dai nada tawagar ta data kunshi sojoji da kuma ma'aikata 1.500, da kuma jiragai marasa matuka da kuma jiragen yaki iri manya da kananan su a kasar Turkiyya wanda daga nan ne take shirya kaddamar da hare-hare kan 'yan ta'ada na Da'esh a Syria.