Kungiyar Kasashen Larabawa Zata Shiga Tsakanin Masar Da Qatar Don Sulhuntawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i8398-kungiyar_kasashen_larabawa_zata_shiga_tsakanin_masar_da_qatar_don_sulhuntawa
Kungiyar kasashen Larabawa zata shiga tsakanin kasar Masar da Qatar.
(last modified 2018-08-22T06:58:37+00:00 )
Jul 20, 2016 10:03 UTC
  • Kungiyar Kasashen Larabawa Zata Shiga Tsakanin Masar Da Qatar Don Sulhuntawa

Kungiyar kasashen Larabawa zata shiga tsakanin kasar Masar da Qatar.

Babban sakatarin kungiyar kasashen Larabawa ya bayyana cewa idan gwamnatocin kasashen Masar da Qatar a shirye suke su maida hulda a tsakaninsu kungiyar a shirye take ta shiga tsakani. Kamfanin dillancin labaran IRNa na kasar Iran ya nakalto Ahmad Abul-gaita yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa kungiyar ba zata nuna wani fifiko a tsakanin kasashen biyu ba don tabbatar da cewa sun dawo da dangantakar da ke tsakaninsu kamar yadda yake a da.

Kasashen biyu sun fara kai ruwa rana a tsakaninsu ne bayan da gwamnatin kasar Qatar ta bayyana goyon bayanta ga kungiyar Ikhwanul musulmin wacce aka haramta a kasar Masar bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yiwa gwamnatin Mohamad Mursi juyin mulki a shekara ta 2013.

Har'ila ila yau Abul=gaita yabukaci kasar Turkia ta gaggauta maido da zaman lafiya a kasar bayan juyin mulkin da bai sami nasara ba don idan wannan halin ya ci gaba zai bar mummunan tasiri ga kasashen yankin.