Tsagerun Yahudawan Sahayoniyya Sun Sake Mamaye Masallacin Qudus
Tsagerun Yahudawan Sahayoniyya sun sake kai farmaki kan Masallacin Aksa da ke birnin Qudus a yau Alhamis, inda suka kutsa kai cikin Masallacin ta Bubul-Magharibah kuma sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun hana duk wani bapalasdine kusantar Masallacin.
Rahotonni sun bayyana cewa; A yammacin yau Alhamis wasu gungun Yahudawan Sahayoniyya 'yan kaka gida sun kai farma kan Masallacin Aksa da ke birnin Qudus, inda suka kutsa cikin Masallacin bisa kariyar sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta hanyar Bubul-Magharibah.
Har ila yau a bayan shigar Yahudawan na Sahayoniyya sun farma al'ummar musulmi da suke cikin Masallacin sakamakon kabbara da musulmin ke yi lamarin da ya haifar da hargitsi a tsakanin bangarorin biyu, kuma sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun hana al'umma kai dauki Masallacin.