Mutanen Birnin Sirt Na Kasar Libya Sun Fara Komawa Gidajensu
Mutanen birnin Sirt a kasar Libya sun fara komawa gidajensu.
A dai dai lokacinda sojojin kasar Libya suke kara samun galaba a kan mayakan kungiyar Daesh a birnin Sirt na kasar Libya mutanen birnin sun fara dawowa gidajensu. Tashar Television ta Euronews ta bayyana cewa a lokacinda maykan kungiyar Daesh ta kwace iko da birnin a cikin watan Yuni shekara 2015 kimanin kashi 3/4 na mutanen garin sun bar gidajensu.
A halin yanzu dai sojojin kasar ta Libya tare da taimakon sojojin majalisar dinkin duniya suna ci gaba da samun galaba a kan mayakan na Daesh. Har'ila yau sojojin kasar ta Libya suna binciken gida gida don tabbatar da dukkan mayakan Desh sun fice daga binin. A cikin watan Yuli na wannan shekara na sojojin kasar ta Libya suka far yiwa mayakan Daesh kofar rako a biniam na Sirt. Tun cin shekara ta 2011 mayakan Daesh suka fara share wuri don mamayar birnin na bkin nruwa.