Hasanain Haykal Na Kasar Masar Ya Rasu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i904-hasanain_haykal_na_kasar_masar_ya_rasu
Shahararren Dan Jaridar Kasar Masar Hassanin Haykal Ya Rasu Yana Da Shekaru 92
(last modified 2018-08-22T06:57:49+00:00 )
Feb 17, 2016 09:06 UTC
  • Hasanain Haykal  Na Kasar Masar Ya Rasu

Shahararren Dan Jaridar Kasar Masar Hassanin Haykal Ya Rasu Yana Da Shekaru 92

Tashar Telbijin din gwamnatin Kasar Masar ta sanar da mutuwar Shahararren dan jaridar kasar Muhammad Hassanain Haykal a yau talata.

Hasanain Haykal wanda ya ke da shahara a tsakanin kasashen larabawa da ma duniya baki daya ya rasu yana da shekaru 92.

A lokacin da ya ke a raye, ya rike shugabancin jaridar ahram ta masar, sannan kuma ya rike mukamin minista a karkashin gwamnatin Gamal Abdunnasir a 1970.

Bugu da kari, Haykal ya rubuta littatafai masu yawa, mafi shahararsu shi ne littafi "Mada'fiu Ayatullah." Akan juyin juya halin musulunci ta Iran.