-
Ranar Talata Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Zata Fara Aiki A Yemen
Dec 17, 2018 10:38Majiyoyi daga MDD, sun bayyana cewa a gobe Talata ne yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin bangarorin dake rikici a Yemen zata fara aiki.
-
An Cimma Yarjejeniya Tsakanin 'Yan Yemen
Dec 14, 2018 04:22Majalisar Dinkin Duniya ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yankunan dake fama da rikici a Yemen, bayan tattaunawar neman zaman lafiya data gudana a Swiden tsakanin bangarorin dake rikici a kasar ta Yemen.
-
MDD : Guteress Zai Halarci Taron Sasanta 'Yan Yemen
Dec 12, 2018 05:24A wani mataki na karfafa wa tattaunawar neman sulhu da ake tsakanin bangarorin dake rikici a kasar Yemen, sakatare Janar na MDD, Antonio Guteres, zai je Swiden domin ganawa da bangarorin da batun ya shafa.
-
Turkey Ta Ce Tana Tattaunawa Da MDD Kan Binciken Kashe Khashoggi
Dec 11, 2018 16:23Kasar Turkiyya ta bayyana cewar tana tattaunawa da Majalisar Dinkin Duniya dangane da batun gudanar da bincike kan kisan gillan da aka yi wa dan jaridar nan dan kasar Saudiyya, Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyan da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyyan.
-
Kudirin Amurka Na Yin Allawadai Da Hamas Ya Ki Karbuwa A MDD
Dec 07, 2018 04:15Kudirin da Amurka ta gabatar na bukatar yin allawadai da kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas, ya kasa samun karbuwa a majalisar dinkin duniya.
-
Tawagar MDD Na Neman Sojojinta 2 A Congo
Dec 06, 2018 09:41Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriya Demuradiyar Congo, ta ce tana neman wasu sojojinta biyu da suka bata tun a watan Nuwamba a yayin wani fada a jihar Beni dake gabashin kasar.
-
Burundi Ta Bukaci Rufe Ofishin MDD, Na Kare Hakkin Bil Adama A Bujumbura
Dec 06, 2018 09:24Gwamnatin Burundi ta bukaci a rufe ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da harkokin kare hakkin bil adama dake Bujumbura, babban birnin Kasar.
-
Yemen : 'Yan Houthis Sun Gindaya Sharadi Kafin Shiga Tattaunawa
Nov 30, 2018 04:18'Yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsis a Yemen, sun gindaya sharadin cewa, zasu shiga tattaunawar da za'ayi a Sweden, a shiga tsakanin MDD, muddin aka basu tabbaci akan tafiyarsu da dawowarsu tawagarsu cikin cikaken tsaro.
-
Kungiyar Red Crescent Ta Iran Ta Sanar Da Aniyarta Na Taimakawa Al'ummar Yemen
Nov 23, 2018 10:16Babban sakataren kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar Iran, Muhammad Muhammadi Nasab ya bayyana aniyar kungiyar ta su ta kasantuwa a kasar Yemen don ba da agaji na gaggawa ga al'ummar kasar Yemen din da suke fuskantar matsaloli na rayuwa sakamakon ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da Saudiyya da kawayenta suke kai wa kasar.
-
Yemen : An Bukaci Masu Rikici Su Nisanci Asibitin Hodeida
Nov 23, 2018 03:50Mukadashin babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, kan harkokin jin kai, Mark Lowcock, da kuma babbar Daraktar asusun kula da yara na MDD, Unicef, Henrietta Fore, sun bukaci masu rikici a kasar Yemen dasu nisanci babban asibitin al-Thawrah na Hodeida.