Dec 06, 2018 09:24 UTC
  • Burundi Ta Bukaci Rufe Ofishin MDD, Na Kare Hakkin Bil Adama A Bujumbura

Gwamnatin Burundi ta bukaci a rufe ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da harkokin kare hakkin bil adama dake Bujumbura, babban birnin Kasar.

Wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Burundi ya shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, tuni gwamnatin ta mika wa babban jami'in MDD a kasar wasikar bukatar rufe ofishin, domin gabatar da ita ga babban kwamishinan MDD kan harkokin kare hakkin bil adama dake Geneva. 

Wasikar ta bukaci da a kwashe dukkan ma'aikatan ofishin ba tare da wata-wata ba, sannan ofishin na da wa'adin nan zuwa watanni biyu domin rufe kofofinsa.

Dama dai tun a watan Oktoba na shekara 2016 ne, gwamnatin ta Bujumbura ta dakatar da aikin ofishin.

 

Tags