Pars Today
Jam'iyyar Rafah ta kasar Mauritaniya ta yi Allah wadai da bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan yankin Zirin Gaza na Palasdinu.
Wani matashin Bapalasdine ya farma sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da wuka a birnin Qudus, inda ya jikkata sojoji biyar, sannan ya yi shahada sakamakon harbinsa da bindiga.
Palasdinawa biyu ne suka yi shahada a lokacinda sojojin HKI suka kai hare-hare kan yankin Gaza na kasar Palasdinu da aka mamaye a yau Talata
Wani bapalasdine ya yi shahada sakamakon harin wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan yankin Zirin Gaza na Palasdinu.
Majiyoyin gwamnatin Palastine sun ce; tun daga lokacin da Trump ya shelanta birnin Qods a matsayin babban birnin Isra’ila ya zuwa yanzu Falastinawa 316 ne suka yi shahada.
Jirgin saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya yi luguden wuta kan wasu Palasdinawa a garin Deir-al-Balah da ke yankin Zirin Gaza lamarin da ya yi sanadiyyar shahadar Palasdinawa uku.
Ma'aikatar harkokin wajen hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa ta yi Allah wadai da shirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na gina dubban gidajen Yahudawan Sahayoniyya a gabashin birnin Qudus.
Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun harbe matashin ne a kusa da haramin annabi Ibrahim (a.s) a tsakiyar garin al-khalil da ke kudancin kogin jOrdan.
Amurka ta sanar da cewa zata hade ofishin wakilcinta na Palasdinu waje guda da ofishin jakadancinta na Isra'ila dake birnin Qudus, kamar yadda ministan harkokin wajen Amurkar Mike Pompeo ya sanar a yau.
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan daliban jami'a a arewacin garin Ramallah, inda suka jikkata Palasdinawa masu yawa.