Bapalasdine Guda Ya Yi Shahada A Garin Al-Khalil
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i33762-bapalasdine_guda_ya_yi_shahada_a_garin_al_khalil
Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun harbe matashin ne a kusa da haramin annabi Ibrahim (a.s) a tsakiyar garin al-khalil da ke kudancin kogin jOrdan.
(last modified 2018-10-23T18:53:02+00:00 )
Oct 23, 2018 18:53 UTC
  • Bapalasdine Guda Ya Yi Shahada A Garin Al-Khalil

Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun harbe matashin ne a kusa da haramin annabi Ibrahim (a.s) a tsakiyar garin al-khalil da ke kudancin kogin jOrdan.

"Yan sahayoniyar sun riya cewa matashin Bapalasdinan ya yi kokarin sarin wani soja ne da wuka.

Sau da yawa sojojin Sahayoniya suke harbe Palasdinawa suna masu riya cewa za su kai hari da wukake akan sojoji ko 'yan share wuri zauna.

Wani labarin daga Palasdinu ya ambaci cewa; Sojojin haramtacciyar Kasar Isra'ila sun kai hari akan Palasdinawa a mashigar Kalandiya.

A kowace rana ta Allah, 'yan sahayoniya suna kai hari ko kuma kama Palasdinawa a yankunan daban-daban na yammacin kogin Jordan.