Kimanin Yan Ta'adda 5000 Ne Suke Kai Kawo Cikin Kasashen Turai
Shugaban yansandan tarayyar Turai- Europol-ya bayyana cewa kimani yan ta'adda 5000 ne suke kai kawo a cikin tarayyar Turai kuma a ko da yauce suna iya kai hare hare a cikin kasashen tarayyar.
Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Wain Rost yana fadar haka a wani hirar da ta hada shi da tashar television ta Rasha today a jiya Lahadi.
Shugaban yansandan ya kara da cewa tun lokacinda aka fara yakin basasa a kasashen Syria da Iraqi a shekara ta 2011 yan ta'adda daga kasashen waje kimani dubu 25-30 ne suka ciga wadan nan kasashen kuma kashi 21% daga cikinsu yan kasashen tarayyar Turai ne. Shugaban yan sandan ya kara da cewa a halin yanzu tarayyar ta turai tana cikin hatsari fadawa cikin hare haren wadan yan ta'adda da suka dawo gida daga kasashen Iraqi da Siria, wadanda kuma suke kai kawonsu cikin kasashen ba tare da wani ya ganesu ba.