Majalisar Dattawan Brazil Ta Goyi Bayan Tsige Dilma Rousseff
Majalisar dokokin Brazil ta kada kuri'ar tsige Shugaba Dilma Rousseff, wace aka jima ana ta cece-kuce akan zarginta da almudahana a kasafin kudin kasar, koda yake Madam Roussef tana musunta zargin.
Kashi biyu cikin uku ne da ake bukata na sanatocin majalisar suka kada kuri'ar tsige Madam Roussef wanda ya kawo karshen shekara 13 da jam'iyyarta ta Workers Party ta yi a kan mulki, koda yake madam Roussef ta bayyana tsige ta da cewa juyin mulki ne.
Tuni dai aka nada Michel Temer wanda ke rike da shugabancin kasar na wucin gadi bayan an dakatar da madam Rousseff a cikin watan Mayu, a matsayin shugaban kasar har zuwa karshen wa'adinta a shekarar 2018.
A zamen sabuwar gwamnatinsa Mr Temer dan shekaru 75 ya yi alkawarin maido da martabar kasar daya daga cikin manyan kasashen yankin latin Amurka.
Saidai bisa ga dukkan alamu matakin baiyi wa wadansu kasashen yankin irinsu Venezuella dadi ba, wace tini ta kirayi jakadanta tare da rage karfin alakarta da kasar ta Brazil.
A wani labari kuma ima ma gwamnatin ta Brazil ta dau matakin kiran jakadanta a '' Carakas'' tare da bayyana takaicin wasu jin wasu kalamai data kira na rashin fahimtar juna daga gwamnatocin kasashen Bolivia, Equador da kuma Cuba.