Koriya Ta Arewa Ta Sake Harba Makamai Masu Linzami
https://parstoday.ir/ha/news/world-i10600-koriya_ta_arewa_ta_sake_harba_makamai_masu_linzami
Shughaban kasar Koriya ta Arewa Pyongyang ya sake harba wasu makamai masu linzami uku a safiyar wannan Litinin.
(last modified 2018-08-22T06:58:52+00:00 )
Sep 05, 2016 01:22 UTC
  • Koriya Ta Arewa Ta Sake Harba Makamai Masu Linzami

Shughaban kasar Koriya ta Arewa Pyongyang ya sake harba wasu makamai masu linzami uku a safiyar wannan Litinin.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kasar ta harba wani makami makamacin wadanan tun daga kasan ruwa a makwani biyu da suka gabata.

An dai harba makaman ne a misalin karfe uku agogon GMT a yankin Hwangju a yammcin kasar a cewar ma'aikatar tsaron kasar Koriya ta Arewar. 

Kawo yanzu dai a cewar labarin ba'a kai ga tantanci irin kirar makamin da Koriya ta Arewa ta harba a wannan safiyar.

Wannan dai shi ne karo na 20 da kasar ke harba makami mai linzame cikin wannan shekera, kuma hudu daga cikinsu shugaba  Pyongyang ne ya harba su da kan shi.

harba makaman na wannan karo na zuwa ne sa'o'i kadan bayan wata ganawa da shugabar kmakofciyyar kasar wato Koriya ta Kudu Park Geun-Hye da shugaba Xi Jinping na Sin a daura da taron G 20.

kwamitin tsaro na MDD dai ya jima yana allawadai da irin wannan matakin na koriya ta Arewa.