Gwatemala : Zabtarewar Kasa Ta Kashe Mutane 9
Jami'an agaji a kasar Guwatemala sun sanar da cewa mutane akalla tara ne suka rasa rayukansu sakamakon zabtarewar kasa bayan ruwan sama da aka samu masu karfin gaske a kudancin babban birnin kasar.
Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu akwai wani mutun guda daya bace, kana akwai wasu mutane 45 da lamarin ya shafa.
Zabtarewar kasar dai ta auku ne a cikin daren jiya Talata wayewar wwannan safiyar Laraba a birnin Nueva dake kudancin babban birnin kasar.
kafin nan jami'an kwana kwana a kasar sun sanar a shafinsu na twiter cewa suna neman wani yaro daya bata.
Lokacin damuwa a wannan kasa ta Gwatemala yana kamawa daga watan Mayu zuwa Satumba, aman so tarin yawa yakan zuwa da yanayi mai cikeda bala'i, inda ko a shekara data gabata mutane 290 suka rasa rayukansu a cikin irin wannan yanayi na zabtarewar kasa daya rusa da wata unguwa a gabashin babban birnin kasar.