Amurka ta yi tayin sayarwa Saudiya makamai na $ biliyan 115
https://parstoday.ir/ha/news/world-i10774-amurka_ta_yi_tayin_sayarwa_saudiya_makamai_na_biliyan_115
Shugaban kasar Amurka ya yi tayin sayarwa masarautar Saudiya makamai na $ bilyan 115
(last modified 2018-08-22T06:58:54+00:00 )
Sep 08, 2016 06:22 UTC
  • Amurka ta yi tayin sayarwa Saudiya makamai na $ biliyan 115

Shugaban kasar Amurka ya yi tayin sayarwa masarautar Saudiya makamai na $ bilyan 115

Tashar telbijin din Press Tv dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto William Hartung na cibiyar siyasar kasa da kasa a Amurka cikin wani rahoto da ya watsa, na cewa Gwamnatin Barak Obama ta yi wa masarautar Saudiya tayin saida mata  makamai da kimarsu ta kai $ biliyan 115, kuma wannan shi ne babban tayi da Amurkan ta yi wa Saudiya cikin shekaru 71.

Rahoton ya ce wannan tayi na gumshe ne cikin kudiri 42, da har yanzu wani bangaren ba a turawa magabatan saudiyar ba.makaman da Amurka ke son sayarwa Saudiyan na iya zama sanadi na matsin lamba ga magabatan birnin Riyad , ganin cewa kungiyar nan mai kula da makamai ta Duniya ta bayyana adawarta da sayarwa duk wata kasar da take taimakawa 'yan ta'adda  makamai domin kasashen Faransa, Birtaniya gami da Amurka sun sanya hannu kan wannan yarjejjeniya a shekarar 2014, kuma matukar Amurka ta aiwatar da wannan mu'amala ta karya  wannan yarjejjeniya.

A bangare guda, masu rajin kare hakin bil-adama sun gudiri aniyar gudanar da zanga-zanga a birnin Watsinton na Amurka domin nuna adawarsu kan wannan kudiri na sayarwa Saudiya da makamai.