Siriya : Kery Da Lavrov Zasu Gana A Geneva
A yau Juma'a ne ake sa ran sakatarorin harkokin wajen kasashen Amurka da Rasha, zasuyi wata ganawa a Geneva da zumar cimma matsaya guda akan yadda za'a shawo kan rikicin kasar Siriya.
Wannan yunkurin kasashen biyu na zuwa ne bayan shafe watanni ba tare da cimma wata matsaya ba akan yadda zasu fahimci juna wajen shawo kan rikicin kasar Siriya.
Amurka da Rasha da ko wannensu keda nasa bangare a rikicin da ake shafe sama da shekaru biyar anayi a wannan kasa ta Siriya na neman yadda zasu farfado da shirin zamen lafiya da kasashen duniya suka cimma a karshen shekara 2015.
Shirin dai ya tanadi tsagaita wuta na dogon lokaci, isar da kayan agaji, da kuma batun kafa gwamnatin wucin gadi ta siyasa tsakanin gwamnatin Siriya da 'yan adawa kasar masu sassaucin ra'ayi.
Wata sanarwa da gwamnatin Amurka ta fitar ta ce tuni sakataren harkokin wajen ta John Kery ya kama hanyar zuwa Geneva inda zai gana da takwaransa Sergio Lavrov a yau Juma'a.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka John Kirby ya fada a cikin sanarwar cewa bangarorin biyu zasu zurfafa batutuwan da suka shafi yadda za'a samu sassauci a rikicin kasar Siriya da fadada shirin isar da kayan agaji ga Siriyawa da kuma ci gaba a yunkurin samun fafita ta siyasa domin kawo karshen yakin basasa daya daidaita wannan kasar ta Siriya..
Ko baya ga hakan wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce, mayan jami'an kasashen biyu sun tattauna ta wayar tarho a jiya Alhamis akan yadda zasuyi hadin gwiwa domin murkushe kungiyoyin 'yan ta'adda a Siriya .